A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, ana gabatar da jerin bahasin Mahdawiyya mai taken "Zuwa ga Al'umma Mai Manufa", da nufin yaɗa koyarwa da ma'arifan da suka shafi Imam Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa), ga masu karatu masu daraja.
A kashi biyu da suka gabata, mun yi ɗan taƙaitaccen bayani kan nauyin da ya rataya a wuyan mata gaba ɗaya, da kuma muhimmin nauyi na musamman da suke da shi wajen tabbatar da manufofin Allah da kuma shimfiɗa hanyar bayyanar Mai Ceton bil'adama. A wannan kashi, za mu amsa tambayoyi biyu da suka shafi matsayi da rawar mata a lokacin bayyanar da mulkin Imam Mahdi (A.F).
Shin akwai mata a cikin mataimaka 313 na sahabban Imam Mahdi (A.S.) na musamman?
A cikin wani dogon hadisi da Jabir ya ruwaito daga Imam Muhammad al-Bakir (A.S.), an ce:
«وَ اَللَّهِ ثَلاَثُمِائَةٍ وَ بِضْعَةَ عَشَرَ رَجُلاً فِیهِمْ خَمْسُونَ اِمْرَأَةً یَجْتَمِعُونَ بِمَکَّةَ عَلَی غَیْرِ مِیعَادٍ.»
"Wallahi, mutane ɗari uku da goma sha uku ne za su zo, kuma a cikinsu akwai mata hamsin. Za su taru a Makka ba tare da wata yarjejeniya ta farko ba." (Tafsirin Ayyashi, Juzu'i na 1, shafi na 65).
Abin lura a cikin wannan ruwaya shi ne, akwai fahimta guda biyu game da kalmar "a cikinsu (فِیهِمْ)":
Fahimta ta farko ita ce, mata hamsin suna cikin adadin mutane 313.
Fahimta ta biyu kuwa ita ce, mata hamsin ɗin za su kasance tare da mutane 313, ba wai suna cikin adadinsu ba.
Wani abin lura kuma shi ne cewa wannan ruwaya tana cikin Tafsirin Ayyashi, kuma kasancewar hadisan da Ayyashi ya ruwaito mursal ne, ya rage ƙarfin hujjar wannan littafi. (Hadisi mursal yana nufin hadisin da ba a ambaci isnadinsa ko maruwaitansa ba.)
An kuma kawo wannan hadisin tare da isnadi a cikin littafin Ghaybat Al-Nu'umani, amma ba tare da jumlar: "A cikinsu akwai mata hamsin." Ba a kuma samu wannan jumla ba a cikin littafin Ikhtisas na Sheikh al-Mufid.
Wani abin lura kuma shi ne, bisa ga shaidu da ke cikin ruwayoyi, kalmar "rajul" tana nufin namiji, ba mace ba.
An kuma kwatanta sahabban Imam Mahdi (A.S.) da:
Sahabban Yaƙin Badar, inda aka ce:
«یَجْمَعُ اَللَّهُ عَزَّ وَ جَلَّ لَهُ مِنْ أَقَاصِی اَلْبِلاَدِ عَلَی عَدَدِ أَهْلِ بَدْرٍ ثَلاَثَمِائَةٍ وَ ثَلاَثَةَ عَشَرَ رَجُلاً.»
"Allah zai tara masa mutane 313 daga sassa daban-daban na duniya, daidai adadin mutanen Badar." (Kamaluddin wa Tamam al-Ni'imah, shafi na 264).
Haka kuma an kwatanta su da sahabban Annabi Ɗalut (A.S.), inda aka ce:
«اَلْقَلِیلُ اَلَّذِینَ لَمْ یَشْرَبُوا وَ لَمْ یَغْتَرِفُوا ثَلَثَمِائَةٍ وَ ثَلَثَةَ عَشَرَ رَجُلاً.»
"Ƙalilan din waɗanda ba su sha ruwan ba kuma ba su ɗiba ba, mutane 313 ne." (Tafsirin Nurus Thaqalayn, Juzu'i na 1, shafi na 248).
A bayyane yake cewa mutane 313 na Yaƙin Badar da kuma na Ɗalut duk maza ne.
Saboda haka, ta fuskar ilimin hadisi, tabbatar da cewa mata suna cikin ko kuma tare da mutane 313 yana da wahala, domin hadisi guda ɗaya ne kawai ya yi nuni da hakan, kuma shi ma mursal ne. A gefe guda kuma akwai ingantattun ruwayoyi da suka nuna cewa adadin 313 ya shafi maza ne kaɗai.
Sai dai, bisa ga bayanan da suka gabata da kuma waɗanda za su biyo baya, rashin kasancewar mata cikin mutane 313 bai taɓa nuna cewa an raina matsayi da darajar mata ba. Domin bayan waɗannan mutane na farko, akwai tarin mataimaka da za su shiga sahun Imam Mahdi (A.F.) a matakai daban-daban, kuma adadinsu ba zai iya ƙididdiguwa ba. Don haka mata za su kasance suna da muhimmiyar rawa da matsayi na musamman a bayyanar da gwamnatin Mahdawiyya.
Shin akwai mata a cikin waɗanda za su yi raj'a (komawa duniya)?
A cikin wannan bincike, ba mu da niyyar tattauna matakin da mata za su yi raj'a a cikinsa, ko kuma ainihin adadin matan da za su yi raj'a, ko cikakkun sunayensu. Abin da yake da muhimmanci shi ne asalin batun raj'ar mata; wato cewa a tsawon tarihi akwai kuma za a ci gaba da samun mata waɗanda suka kai kololuwar matsayi na imani da sanin Allah, har Allah Ya ba su damar yin raj'a da kuma kasancewa tare da Hujjar Allah na ƙarshe.
Imam Ja'afar as-Sadiƙ (A.S.) ya ce a cikin wata ruwaya:
یُکَرُّ مَعَ اَلْقَائِمِ (عَلَیْهِاَلسَّلاَمُ) ثَلاَثَ عَشْرَةَ اِمْرَأَةً. قُلْتُ: وَ مَا یَصْنَعُ بِهِنَّ؟ قَالَ: یُدَاوِینَ اَلْجَرْحَی، وَ یَقُمْنَ عَلَی اَلْمَرْضَی، کَمَا کَانَ مَعَ رَسُولِ اَللَّهِ (صَلَّی اَللَّهُ عَلَیْهِ وَ آلِهِ). قُلْتُ: فَسَمِّهِنَّ لِی. فَقَالَ: اَلْقِنْوَاءُ بِنْتُ رُشَیْدٍ، وَ أُمُّ أَیْمَنَ، وَ حَبَابَةُ اَلْوَالِبِیَّةُ، وَ سُمَیَّةُ أُمُّ عَمَّارِ بْنِ یَاسِرٍ، وَ زُبَیْدَةُ، وَ أُمُّ خَالِدٍ اَلْأَحْمَسِیَّةُ، وَ أُمُّ سَعِیدٍ اَلْحَنَفِیَّةُ، وَ صُبَانَةُ اَلْمَاشِطَةُ، وَ أُمُّ خَالِدٍ اَلْجُهَنِیَّةُ.
"Tare da Al-Qa'im (A.S.), mata goma sha uku za su yi raj'a." Sai na tambaya: "Wane aiki za a ba su?" Sai Imam ya ce: "Za su yi jinyar waɗanda suka ji rauni, kuma za su kula da marasa lafiya, kamar yadda suka kasance tare da Manzon Allah (S.A.W.A) suna yin hakan." Sai na ce: "Ka ambaci sunayensu gare ni." Sai Imam ya ce: "Qanwa'u 'yar Rashid, Ummu Ayman, Hubabah al-Walibiyya, Sumayya mahaifiyar Ammar bn Yasir, Zubayda, Ummu Khalid al-Ahmasiyya, Ummu Sa'id al-Hanafiyya, Subanah mai gyaran gashi, da Ummu Khalid al-Juhaniyya." (Dala'ilul Imamah, Juzu'i na 1, shafi na 484).
A wasu littattafai ma an ambaci adadi da sunayen wasu matan da za su yi raj'a. (Kamar yadda muka bayyana, sunayensu, adadinsu da lokacin raj'arsu ba su ne batunmu ba.)
Abin da ya fi muhimmanci, kuma zai iya taimaka wa mata wajen tafiya a kan hanyar addini, neman ilimi da sanin Allah, da kuma tabbata a kan addinin Allah, shi ne yin nazari a kan siffofin waɗannan mata da aka ambata a cikin ruwayoyi. Za mu yi ishara ne kawai zuwa wani ɓangare daga cikinsu.
'Yanci, tsayin daka da juriya a gaban rundunar ƙarya, su ne mafi muhimmancin siffofin da suka haɗa waɗannan mata masu raj'a.
Labarin Subanah, mai gyaran gashin 'yar Fir'auna
Manzon Allah (S.A.W.A) ya ce game da Subanah, mai gyaran gashin 'yar Fir'auna:
"Lokacin da aka kai ni Mi'iraji, na ji wani ƙamshi mai daɗi ƙwarai. Sai na ce wa Jibrilu: 'Wane ƙamshi ne wannan?' Sai ya ce: 'Wannan ƙamshin mai gyaran gashin iyalan Fir'auna da 'ya'yanta ne. Tana taje gashin 'yar Fir'auna ne sai matsefin ya faɗi daga hannunta, sai ta ce: "Bismillah." Sai 'yar Fir'auna ta ce: "Ki na nufin mahaifina ne?" Sai matar ta ce: "A'a, ina nufin Ubangijina, Ubangijinki da kuma Ubangijin mahaifinki." Sai 'yar Fir'auna ta ce: "Lallai zan gaya wa mahaifina." Matar ta ce: "Ki faɗa masa." Sai ta gaya wa mahaifinta. Fir'auna ya kira matar tare da 'ya'yanta, ya ce: "Wane ne Ubangijinki?" Sai ta ce: "Ubangijina da Ubangijinka Allah ne." Sai Fir'auna ya ba da umarni a ƙera wani murhu na tagulla aka hura shi sosai. Sannan ya kawo matar da 'ya'yanta. Sai matar ta ce: "Ina da wata buƙata a gare ka." Ya ce: "Menene?" Ta ce: "Ka tattara ƙasusuwana da na 'ya'yana ka binne su." Sai ya ce: "Saboda alherin da kika taɓa yi mana, zan yi miki wannan." Daga nan ya ba da umarni aka riƙa jefa 'ya'yanta ɗaya bayan ɗaya cikin murhun har aka kai ga ƙaramin ɗanta wanda ale shayarwa. Sai jaririn ya yi magana ya ce: "Ya Uwata! Ki yi haƙuri, domin kina kan gaskiya." Bayan haka aka jefa matar tare da jaririnta cikin murhun." (Bihar al-Anwar, Juzu'i na 13, shafi na 163).
Game da Sayyida Sumayya, mahaifiyar Ammar
Game da Sayyida Sumayya, mahaifiyar Ammar bn Yasir, an ruwaito cewa:
«وَ کَانَتْ مِمَّنْ تُعَذَّبُ فِی اَللَّهِ لِتَرْجِعَ عَنْ دِینِهَا فَلَمْ تَفْعَلْ فَمَرَّ بِهَا أَبُو جَهْلٍ فَطَعَنَهَا فِی قَلْبِهَا فَمَاتَتْ.»
"Ta kasance cikin waɗanda aka azabtar saboda Allah domin su bar addininsu, amma ba ta yi haka ba. Sai Abu Jahl ya wuce ta, ya soke ta a zuciya, kuma ta rasu." (Biharul Anwar, Juzu'i na 18, shafi na 241).
Ita (Sumayya) tana daga cikin mutanen da aka azabtar saboda Allah domin ta yi ridda daga addininta, amma ta ƙi. Sai Abu Jahl ya zo ya soke ta a zuciya da makami, har ta yi shahada.
Akwai kuma wasu misalai da dama makamantan wannan.
Abin Lura
Yanayi da halin da mutum yake ciki na ɗaya daga cikin hujjojin da wasu mutane, musamman mata, suke bayarwa wajen bayyana dalilin raunin imaninsu da rashin zurfin saninsu na addini. Amma idan aka yi nazari a rayuwar mata masu gina tarihi a Musulunci, za a fahimci cewa a tafarkin cimma manufofin Allah da kusantar Mahalicci, babu wani mutum ko wani yanayi da zai iya hana mutum kaiwa ga burinsa.
Allah Maɗaukakin Sarki a cikin Alƙur'ani mai girma, lokacin da Ya ambaci Sayyida Asiya (A.S.), bai kira ta da sunanta ba. Maimakon haka Ya kira ta da: "Matar Fir'auna."
Wannan domin Ya jawo hankalin dukkan maza da mata muminai cewa, ita ta kasance cikin fadar mafi girman azzalumin zamaninta, ba tare da wani mataimaki face Allah ba, amma duk da haka ta zama abin koyi ga kowa.
Kalmar Ƙarshe
Raj'a ba ta taƙaitu ga mutanen da suka gabata kaɗai ba, har ma ta shafi waɗanda za su zo nan gaba. Saboda haka ne aka ƙarfafa mana karanta Du'ar Ahd, inda ake cewa:
«اللَّهُمَّ إِنْ حَالَ بَینِی وَ بَینَهُ الْمَوْتُ الَّذِی جَعَلْتَهُ عَلَی عِبَادِک حَتْما مَقْضِیا، فَأَخْرِجْنِی مِنْ قَبْرِی مُؤْتَزِرا کفَنِی شَاهِرا سَیفِی مُجَرِّدا قَنَاتِی مُلَبِّیا دَعْوَةَ الدَّاعِی فِی الْحَاضِرِ وَ الْبَادِی.»
"Ya Allah! Idan mutuwar da Ka wajabta wa bayinka ta raba ni da shi (Imam Mahdi A.F.), to Ka fito da ni daga kabarina ina sanye da likkafanina, ina zare takobina, ina riƙe da mashina, ina amsa kiran mai kira a cikin birane da ƙauyuka."
Hakika, domin mutum ya kai ga wannan matsayi mai girma, dole ne ya ƙawata kansa da siffofin da ruwayoyi suka ambata game da masu raj'a.
A wannan tafarki kuwa babu wani bambanci tsakanin namiji da mace.
Ra'ayinka